Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Jami'an tsaron Bahrain sun cafke wani dan kasar nan bayan sun kai samame a gidansa da ke kauyen Abu Quwa. Ba a san dalilin kame wannan dan kasar Bahrain mai suna Sayyid Muhammad Sayyid Majid ba.
Hakazalika, kauyuka da dama a kasar Bahrain da suka hada da Al-Draz da Al-Sanabs da kuma Karzkan sun gudanar da zanga-zangar neman a sako fursunonin siyasa wadanda rayuwarsu ke cikin hadari. Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken tare da jaddada hadin kai ga fursunonin siyasa a Bahrain.
@abna24